Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Uhuru Kenyatta na kan gaba da kashi sama da 55% a kri'un da aka kada a zaben na jiya, inda ya baiwa abokin hamayarsa Raila Odinga tazara ta kusan kuri'u miliyan daya da rabi.
Mista Odinga wanda sakamakon ya ce ya samu kashi kusan 45%, ya bayyana a wani taron manema labarai a cikin daren jiya cewa alkalumen zaben na bogi ne.
Kafin hakan dai bayanai daga kasar sun ce zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a mafi yawan wurare, a inda ita kuwa hukumar zaben kasar ta yi kira ga jama'ar kasar su kai zuciya nesa su jira sakamakon zaben cikin kwaciyar hankali.
Jama'a dai a kasar na da fargabar sake barkewar rikicin bayan zabe irin wanda aka yi a shekara ta 2007 wanda ya yi ajalin mutane 1'100 tare kuma da cilastawa wasu 600,000 barin muhallansu.288